Jerin kasashen da suka fi ko ina dadin rayuwa a duniya
- A kwanakin baya majiyar mu Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen da su ka fi ko ina hatsari a duniya, to yau ma ga ta da Jadawalin kasashen da suka fi ko ina dadin rayuwa a duniya
Wasu kwararrun masana fannin zaman lafiya da walwalar jama'a na duniya sun bayyana sunan kasar da jama'arta suka fi kowacce al'umma rayuwa cikin jin dadi da walwala.
DUBA WANNAN: Kididdiga ta kara tabbatar da cewa farashin masarufi na kara saukowa a Najeriya
Kwararrun masanan, sun bayyana kasar Finland a matsayin kasar da ta fi kowacce kasa dadin rayuwa a cikin kasashe 156 na fadin duniya, bayan binciken da masanan suka yi kan tsawon rayuwar al'ummar kasar, tallafawa wanda basu da karfi, yaki da cin hanci da rashawa, cigaban kasa, walwalar masu neman wurin fakewa, da dai sauran su.
An bayyana sakamakon zaben kasar a mujallar kasashen da suka fi ko ina dadin zama a duniya wato "The World Happiness Report 2018" a ranar Laraba 14 ga watan Maris na wannan shekarar.
Bayan kasar Finland, kasar da ta ke bi mata ita ce kasar Noway, sai kasar Danmak a matsayin ta uku, kasar Island ta zo a ta hudu, Scotland ta biyar, Holland ta shida, kasar Kanada ta zo a ta bakwai, New Zealand ta zo a ta takwas da kuma kasar Ostereliya a matsayin kasa ta tara.
Kasar Amurka dai ta kasance a matsayin kasa ta 18 a jadawalin sunayen kasashen da al'ummarsu suka fi jin dadi da farin ciki da walwala a fadin duniyar nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng