Sharhi: Sanata a Najeriya ya fi shugabannin kasa irinsu Trump, Theresa May, Vladimir Putin da Angela Merkel yawan albashi
Akwai wani abu a jama’a basu sani ba, shine sanatan Najeriya ya fi sauran yan majalisun duniya irinsa samun albashi. Bal har manyan shugabannin kasan duniya basu kai Sanatan Najeriya albashi ba.
Abin takaicin na da yawa, na daya shine sanatan Najeriya babu wani abin kirkin da yake tabukawa illa amsan miliyoyi a karshen wata.
Ta yaya za’ayi mutum yana karban kudi N13.5 million a wata, kuma ba shikenan ba, zai karbi N750,000 kudin albashi, N200 Million kudin ayyuka (yawanci basu yi), sannan kuma wasu kudade da ba’a san iyakansu ba.
A dalar Amurka ko Fam na turai, kimanin £27, 000 ko $37, 500 kenan.
Game da cewar Metro UK, Albashin Firam ministan Birtaniya £150, 402 ne a shekara. A lissafe, sanatan Najeriya na karban ninki 2 na abinda Firam ministan Birtaniya ke karba a shekara.
Uwa uba shugaban kasar Amurka, Donald Trumo, albashinsa a shekara $400 000. Amma sanatan Najeriya zai hada wannan kudi a kasa da watanni 11, banda na haram da cuwa-cuwa.
Shi kuma shugaban kasan Sin, Xi Jinping, mai karban $20,593, sanatan Najeriya ma zai iya daukan sa aiki.
KU KARANTA: Buhari zai yi ganawan sirri da shugabannin majalisa da daren nan
Mace mafi karfi kuma a duniya, Angela Merkel, na kasar Jamus, albashinta a a wata $21,912. Shi kuma sanatan Najeriya na karban $37, 500 ko wani wata.
Kai a karshe, sanata a Najeriya zai iya biyan shugaban kasan Rasha, Vladimir Putin. Tunda albashin Putin a wata $12,586.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng