Allah Ya kiyaye gaba: Wata wuta da ta tashi a wata kasuwar jihar Kano ta babbaka shaguna 22

Allah Ya kiyaye gaba: Wata wuta da ta tashi a wata kasuwar jihar Kano ta babbaka shaguna 22

Wata gobara ta tashi da safiyar Laraba 14 ga watan Maris a kasuwan yan katako dake unguwar rijiyan lemu na jihar Kano, wanda ta yi sanadiyyar babbaka shaguna 22, inji rahoton majiyar Legit.ng.

Kaakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saidu Muhammed ne ya bayyana ma kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, cewar gobarar ta taso ne da misalin karfe 3:10 na dare.

KU KARANTA: Dakataccen dan majalisa Abdulmuminu ya koma bakin aiki a majalisa bayan kwanaki 108

“Mun samu kira da tsakar daren Laraba daga wani muhammad Yahaya dake unguwar Kurna da misalin karfe 3:10 na dare game da wutar data tashi a kasuwar, jin hakan ya sa jami’anmu suka dira kasuwar don kashe wutar da misalin karfe 3:14.” Inji Saidu.

Allah Ya kiyaye gaba: Wata wuta da ta tashi a wata kasuwar jihar Kano ta babbaka shaguna 22
Gobara

Sai dai Kaakakin yace suna cigaba da gudanar da bincike don tabbatar da musabbabin faruwar gobarar, sa’annan ya shawarci yan kasuwa da su guji amfani da abubuwan da ka iya kawo gobara, don kiyaye gaba.

Bugu da kari Kaakain ya shawarci jama’a da su dinga ajiye bukitin kashe wuta, manyan barguna da na’urar kashe wuta a gidanjensu don rage karfin wutar gobara kafin yan kwana kwana su iso.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: