Yanzunnan: SSANU, NAAT, NASU da sauran masu yajin aiki sun dawo bakin aiki bayan sulhu
- Sun fara yajin aikin tun a bara
- Ma'aikatan dai na neman hakkokinsu
- Yanzu sun janye bayan sulhu, zasu koma aji
Bayan shafe watanni akalla 3 suna yajin aiki, ma'aikatan jami'o'in Najeriya na SSANU, NAAT da NASU a yau sun janye yajin aikinsu wanda shine ya gurgunta harkar ilimin jam'o'in wata da watanni a farkon shekarar nan.
Sanarwar tana zuwa ne bayan da Samson Ugwoke, national chairman na Joint Action Committee dinsu, watau kwamitin hadin gwiwa shine ya fadi hakan a yau laraba, bayan wani zama da sukla yi da hukumomi.
Komawar wani bangare na masu yajin, a makon jiya, ya tayar da hatsaniya tsakanin baangarorin, amma ga alama yanzu sun daidaita.
DUBA WANNAN: Nasarorin Buhari a shekarar nan
Kungiyoyin dai sune ke aiki a jami'a domin tafiyar da su kam ar yadda ya kamata, watau manyan ma'aikata, SSANU, ma'aikata wadanda basu koyarwa, NASU, da kuma NAAT.
A 15 ga wannan watan zasu dawo aikin gaba-daya, sun kuma shiga yajin aikin ne tun 5 ga watan Disamba ta bara.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng