Dansanda ya kashe dalibin makaranta mai shekaru 16 yayin da yake bin masu zanga-zanga

Dansanda ya kashe dalibin makaranta mai shekaru 16 yayin da yake bin masu zanga-zanga

- 'Yansannda jihar Legas sun ceto rayuwar mata daga ake zargin barauniyar yara ce daga hannun fusatattun matasa

- Wani dalibin makaranta ya gamu da ajalinsa yayin da wasu 'yansanda suka biyo masu zanga-zanga a jihar Legas

Harbin da wani dansanda dake aiki da sashen rundunar ‘yansandan Ijora Badia a jihar Legas yayi ya kashe wani dalibin makarantar sakandare mai shekaru 16.

Dalibin makarantar Randle Randle Secondary School dake Apapa, mai suna Emmanuel, ya gamu da ajalin sa ne yayin da fito kofar gidan su dake unguwar Ijora Badia, dan kallon masu gudanar da zanga-zana da ‘yansanda suka biyo su.

Dansanda ya kashe dalibin makaranta mai shekaru 16 yayin da yake bin masu zanga-zanga
Dansanda ya kashe dalibin makaranta mai shekaru 16 yayin da yake bin masu zanga-zanga

Legit.ng ta samu rahoton cewa wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a ofishin ‘yansandan unguwar Ijora Badia a safiyar ranar Lahadi saboda kwato wata mata da ake zargin ta sace karamar yarinya mai shekaru biyar daga hannun matasan a lokacin da suke kokarin kashe ta.

KU KARANTA : Wani mahaukaci ya shiga makarantar Ogun, ya kashe dalibai biyu

Harbin da ‘yansanda suka yi dan korar masu gudanar zanga-zanga a gabam ofishin su yayi sanadiyar mutuwar Emmanuel.

Rundunar ‘yansandan unguwar sun ce sun yi harbi ne saboda matasan sun yi yunkurin daukar doka a hannun su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng