Gwamna Lalong ya kori shugaban karamar hukumar Bokkos
- Gwamnan Lalong ya sanar da korar shugaban karamar hukumar Bokkos Mista Simon Angola ranar Talata
- Lalong ya umarci, Mista Tamai Simon ya maye gurbin Simon Angola a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Bokkos
Gwamnan jihar, Filato, Mista Simon Lalong, ya kori shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Bokkos, Simon Angol, akan cigaba da kashe-kashen da ake yi a yankin.
Gwamnan ya aikawa majalissar Dokokin jihar Filato da wasikar korar Simon Angola ranar Talata, wanda Kakakin majalissar dokokin jihar ya karanta ta 'yan majalissar jihar.
Gwamnan ya zargi shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Bokkos da rashin kawo karshen rikicin da ya addabi yankin.
KU KARANTA : Shugaban kwamitin shirin ciyar da daliban makaranta Frimare na kasa, ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su
A wasikar, gwamna Lalong, ya umarci, Mista Tamai Simon, ya maye gurbin, Mista Simon Angol, a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Bokkos.
Lalong ya ce yana bukatar izinin majalissar dokokin jihar Filato ta amince da, Mista Tamai Simon, a matsayin sabon shugaban hukumar Bokkos.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng