Makiyaya sun hallakar da coci 500 a jihar Benuwe - CAN

Makiyaya sun hallakar da coci 500 a jihar Benuwe - CAN

A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kungiyar kirista ta CAN reshen jihar Benuwe, Rabaran Akpen Leva ya bayyana cewa, rikicin makiyaya ya hallakar da coci fiye da 500 a sassan jihar.

Rabaran Leva ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Makurdi, inda yace rikicin makiyaya da ya fara kunno kai tun a shekarar 2011 ya sanya da yawan masu mabauta sun tsere daga yankunan su.

Babban limamin ya kuma bayyana cewa, baya ga dakunan su na addinai akwai kuma manyan makarantu, asibitoci da gidajen marayu da rikicin ya salwantar.

Makiyaya sun hallakar da coci 500 a jihar Benuwe - CAN

Makiyaya sun hallakar da coci 500 a jihar Benuwe - CAN

Ya ci gaba da cewa, akwai abin takaici tare da kuma tausayawa dangane da lamarin jihar Benuwe, sakamakon yadda rikicin ya rufe gwamnatin jihar cikin rudani.

KARANTA KUMA: Yaki da rashawa: Sai Buhari ya damke Obasanjo za mu san dagaske yake - Kalu

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya damko tsohon shugaban kasa Obasanjo bisa laifukan rashawa da suka afku a gwamnatin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel