An shiga Kotu da wani Bawan Allah da ake zargi ya kashe matar sa da hannun sa
- Wani Mutumi ya hallaka Mai dakin sa da kan sa a Garin Legas
- Yanzu haka an dai wuce da shi gaban Alkali inda ake ta shari’a
- Idan aka same shi da laifi to lallai ta shi ta kare shi ma a Duniya
Ana zargin cewa wani Bawan Allah ya kashe matar sa da hannun sa a wata Anguwa mai suna Ojudu a cikin Garin Legas a wancan watan da ya gabata. Idan an kama sa da laifi shi ma kuwa za a aika sa lahira babu wata-wata.
Kotun Majistare da ke Ebute Meta a Garin Legas ya karbi karar da ake yi na wani Bawan Allah mai suna Godwin Alawa wanda ake zargi da laifin kashe matar sa ta aure. Yanzu haka an daure sa a bayan kanta har a gama shari’a.
KU KARANTA: Za a fanshi wasu 'Yan Najeriya da ke kasar Libya
Ana zargin cewa Mista Godwin Alawa mai shekaru 48 a Duniya ya kashe mai dakin sa Victoria Edet mai shekaru 42 a gidan su da ke Kayin Budland a Unguwar Ojodu a cikin Garin na Legas bayan ya lakada mata mugun duka.
Darektan Hukumar da ke karar masu laifi a Legas watau DPP ya nemi a tsare wannan mutumi. Dama dai bincike ya nuna cewa Alawa ya saba dukan matar ta sa. Alkali Mrs A.O. Komolafe ta nemi a dage shari’a sai tsakiyar watan gobe.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng