Gaba dai gaba dai: Rahama sadau ta samu lambar karramawa na ‘Tauraruwa mai haskawa’ daga majlisar dinkin Duniya UN
- Majalisar dinkin Duniya ta karrama Rahama Sadau
- Majalisar dinkin Duniya ta karrama Rahama a Amurka da lambar yabo
Shahararriyar yar wasan fina finan Kannywood, Rahama Sadau ta samu lambar yabo daga majalisar dikin Duniya, UN, wanda ta karramata da kyautar ‘Tauraruwa mai haskawa’, inji rahoton Daily Trust.
KU KARANTA: Alhamdulillah: Mai martaba Sarkin Zazzau ya dawo daga jinya a kasar Ingila (Hotuna)
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Raham ta bayyana haka ne a shafinta na sadarwa, inda tace majalisar dinkin Duniya ta karramata ne a yayin wani bikin fina finai na Duniya daya gudana a birnin New York na kasar Amurka.
Rahama tace:”An karrama ni a daren jiya, na ji dadi sosai, tare da alfahari da kai na, musamman yadda na yi gogayya da manyan mata na Duniya gaba daya. A irin wannan lokaci, mutum ya kan tambayi kansa, wai ya aka yi na kai ga wannan matsayi? A gaskiya ba zan manta da wannan ran aba har abada.”
Idan za’a tuna, a satin data gabata ne Legit.ng ta kawo maku rahoton yadda jarumar Rahama ta rasa budurcinta tun tana karama, sai dai ba kamar yadda mutane ke tsammani ba, Rahama ta bayyana cewa fyade aka yi mata tun tana karama, a haka ne ta rasa budurcin nata.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng