Yanzun nan: Hukumar shirya jarabawar JAMB ta saki sakamakon jarabawa na 2018

Yanzun nan: Hukumar shirya jarabawar JAMB ta saki sakamakon jarabawa na 2018

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari na kasa, JAMB ta sanar da fara sakin sakamakon jarabawar da dalibai suka zana a jarabawar dake gudana a yanzu, inji rahoton Premium Times.

Dalibai sun fara zana jarabawar na bana ne a ranar juma’a 17 ga watan Maris, inji majiyar ta Legit.ng. Kaakakin hukumar JAMB, Fabian Benjamin ne ya sanar da haka a ranar Talata 13 ga watan Maris.

KU KARANTA: Zaman lafiya: Wasu makiyaya sun mika ma Yansanda bindigunsu guda 30 a jihar Neja

Fabian yace hukumar ta kammala tantance cibiyoyin jarabawar da aka saki sakamakonsu, sa’annan ya shawarci dalibai da su duba shafin hukumar JAMB din don duba sakamakon nasu,: “Za’a dinga sakin sakamakon jarabawar ne rukuni rukuni, kowa zai iya dubawa.”

Yanzun nan: Hukumar shirya jarabawar JAMB ta saki sakamakon jarabawa na 2018

Jarabawar JAMB

Hakazalika, wani dalibi daga jihar Kwara da ya zana jarabawar, Segun Abidoye ya tabbatar da sakin sakamakon, inda yace: “Da tsakar dare aka fara sakin sakamakon, a yanzu haka na samu nawa.”

Tun kafin jarabawar ne majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar JAMB na fadin ba zata yi garajen sakin sakamakon jarabawar ba har sai ta kammala binciken kwakwaf tare da tantance cibiyoyin jarabawar da dalibai suka zana jarabawar ta JAMB

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel