Jirwaye mai kamar wanka: Duba hotunan tarbar da 'yan Peace corps su ka yiwa Buhari a Benuwe
Wasu gungun matasa sun yi jerin gwano sanye da kayan kungiyar nan ta Peace Corps dauke da wasu rubutattun sakonni dake nuna rashin jin dadinsu da watsi da kudirin mayar da kungiyar hukumar tsaro a gwamnatance da shugaba Buhari ya yi duk da amincewar majalisar dattijai.
Jagorori da askarawan kungiyar Peace sun gudanar da zanga-zangar lumana a jiya litinin a garin Makurdi, babban birnin jihar Benuwe, yayin ziyarar shugaba Buhari a jihar.
Matasan, dauke da rubutattun sakonni, sun yi kira ga shugaba Buhari da ya sake duba a kan kudirin da majalisar dattijai ta amince da shi na mayar da kungiyar hukumar tsaro a gwamnatance.
Shugaba Buhari ya yi watsi da bukatar mayar da Peace Corps hukumar tsaro duk da amicewar da majalisar dattijai ta yi, ya na mai bayyana cewar babu bukatar yin hakan a halin yanzu, baya ga rashin kudi da gwamnati zata yi amfani da su domin daukan dawainiyar hukumar
DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa Buhari bai san Sifeton ‘yan sanda ya bijirewa umarninsa ba – Adesina
'Yan majalisar dattijai sun bukaci Buhari ya canja matakinsa a kan hukumar tare da bayyana cewar zasu tabbatar da Peace Corps a matsayin hukumar tsaro idan shugaban ya ki yin hakan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng