Wani mahaukaci ya shiga makarantar Ogun, ya kashe dalibai biyu

Wani mahaukaci ya shiga makarantar Ogun, ya kashe dalibai biyu

- Mahaukaci ya kashe dalibai biyu masu shekaru hudu a jihar Ogun

- Rudnunar 'yansadar jihar Ogun ta ce zata kai mahaukacin da ya kashe alibai asibitin mahaukata dan tabbatar da lafiyar kwakwalwar sa

Wani mutum da ake zargin yana da tabu hankali mai suna, Lekan Adebisi, ya shiga makarantar Frimare na St. John dake unguwar Agodo, a karamar hukumar Waterside a jihar Ogun ya kashe dalibai guda biyu.

Dalibai guda biyu da ya kashe, Mubaraka Kalesowo da Sunday Obituyi, ‘yan Nusiri ne masu shekaru hudu da haihuwa.

Mai laifin ya shiga makarantar ne a lokacin da dalibai makaranatar suka fito hutun tara wato (Break) dan cin abinci.

Wani mahaukaci ya shiga makarantar Ogun, ya kashe dalibai biyu
Wani mahaukaci ya shiga makarantar Ogun, ya kashe dalibai biyu

Rahotanni sun nuna Adebisi wanda sananne ne a unguwar ya gudu daga wurin bayan ya tafka aika-aikan.

KU KARANTA : 'Yan bindiga sun tafka ta'asa a gidan shugaban jam'iyyar PDP da dan majalisa a jihar Kogi

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwan wannan lamari.

Abimbola Oyeyemi, y ace, rundundar ‘yansadan jihar sun fara bincike akan al’amarin, kuma za su kai mai lafin asibitin mahaukata dan tabbatar da lafiyar kwakwalwar sa idan su kama shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng