Ka fada ma Dubai da Birtaniya su wallafa sunayen yan Najeriya da suka mallaki kadarori a kasashensu – Shehu Sani ga Buhari
Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana dacewar a sanar da yan Najeriya sunayen shwuagabanninsu da suka mallaki kadarori a kasashen Birtaniya da Dubai, inji rahoton Daily Trust.
Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na sadarwar zamani, Twitter, inda yace a maimakon gwamnatocin kasashen Birtaniya da Dubai su sanar da gwamnatin Najeriya kadai, kamata yayi su wallafa sunayen ta yadda yan Najeriya zasu san wanene ba wanene ba.
KU KARANTA: A Najeriyar mu: Yadda wani saurayi mai shekaru 23 ya auri kanwarsa mai shekaru 16
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwmanatin Najeriya ta fara musayawar bayanan biyan harajin kadarori a tsakaninta da gwamnatin kasar Dubai da na Birtaniya da nufin sanin su wanene suka mallaki kadarori ta hanyar satar kudin jama’a.
Sanatan ya bayyana cewa don tabbatar da gaskiya da adalci, kamata yayi gwmanatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bukaci a wallafa sunayen barayin gwmanati da suka karkatar da kudaden al’umma kasashen waje.
“Ban goyi bayan gwamnatocin Amurka, Dubai da na Birtaniya su bayyana ma gwamnatin tarayya kadai sunayen yan Najeriya masu mallakan kadarori a kasashensu ba, a’a, nafi son su bayyana sunayen don kowa ya san su.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng