Madalla! Naira ta kara daraja bayan da CBN ya sake malalo $195 miliyan a kasuwar 'yan canji

Madalla! Naira ta kara daraja bayan da CBN ya sake malalo $195 miliyan a kasuwar 'yan canji

Babban bankin Najeriya watau CBN a kokarin da suke na ci gaba da ganin takardar kudin Naira ta kara daraja ya sake malalo kudin kasar waje da suka tasar ma Dala miliyan 195 a kasuwar 'yan canji duk domin karin karfi da darajar Naira din.

A wani labarin kuma, babban darakta Janar na kafar yada labarai ta murayar Najeriya Mista Osita Okechukwu ya bayyana cewa idan ma har shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar zarcewa a zaben 2019, to 'yan kabilar Ibo ne za su fi kowa morewa.

Wannan kalaman na shi dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan kungiyar gamayyar 'yan kabilar Ibo din ta Ohanaeze Ndigbo ta fitar da sanarwar cewa su har yanzu ba su yanke hukuncin wanda za su marawa baya ba a zaben 2019.

Madalla! Naira ta kara daraja bayan da CBN ya sake malalo $195 miliyan a kasuwar 'yan canji
Madalla! Naira ta kara daraja bayan da CBN ya sake malalo $195 miliyan a kasuwar 'yan canji

KU KARANTA: Sanatoci sun bayyana yawan kudaden da suke ansa duk wata

A wani labarin kuma, kawo yanzu dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta bayyana mana cewa kawo yanzu baitul malin kasar Najeriya ta kai dalar Amurka biliyan 43.2, yawan da bata taba yi ba tun kimanin shekaru hudu da suka gabata kamar yadda babban bankin Najeriya ya bayyana a jiya Laraba.

Haka ma dai gwamnan babban bankin Najeriya din Mista Godwin Emefiele ya yi hasashen cewa baitul malin kasar zai iya kaiwa dalar Amurka biliyan 60 kafin shekarar 2019 indai har aka cigaba da tafiya yadda ake yanzu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng