‘Dan adawan Shugaba Buhari yace Shugaban kasar ya ci ya zarce a 2019
- Wani babba a PDP yace yana ganin Buhari ya dace ya nemi tazarce
- Iwuanyawu yace shekarau ba za su hana Shugaban kasar takara ba
- ‘Dan siyasar yace irin su Obasanjo ba za su hana Buhari zarcewa ba
Wani Jigo a Jam’iyyar adawa ta PDP kuma daya daga cikin manya a kasar Inyamurai Emmanuel Iwuanyawu ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kokarin da ya dace ya nemi tazarce musamman idan aka duba lamarin Boko Haram.
Emmanuel Iwuanyawu yana ganin cewa Shugaban kasar yayi namijin kokari a shekaru kusan 3 da yayi yana mulki yace kuma irin su tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ko wani ba su isa su hana Shugaba Buhari neman takara a 2019 ba.
KU KARANTA: Jama'an Benuwe sun gindayawa Shugaba Buhari sharuda
Iwuanyawu yace sai dai kar Shugaban kasar ya biyewa ‘yan kanzagin da ke kokarin zuga sa da ya dauki shawarar su da karfi da yaji. Shi dai Iwaunyawu yace bai yadda da dukkanin abin da Obasanjo ya fada a kan mulkin Buhari ba kwanaki a wasika.
Babban ‘Dan adawan yace har ‘yan shekaru 93 su na takara balle kuma irin su Shugaba Buhari da yake shekara 75. Sai dai Jigon na PDP yace akwai kuma wasu da ke neman tursasa Shugaban kasar har su na cewa za su kai shi Kotu inda bai yi takara ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng