Sheƙe aya a bikin Fatima Ganduje: Sheikh Aminu Daurawa ya wanke kansa dangane da zargin kawar da kai

Sheƙe aya a bikin Fatima Ganduje: Sheikh Aminu Daurawa ya wanke kansa dangane da zargin kawar da kai

Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, kuma fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa ya bara game da cecekucen da ake yi a shafukan sadarwa na yanzar gizo inda ake zargin Hisbah da kawar da kai daga sheke ayar da aka yi a bikin diyar Ganduje.

Malam Daurawa ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, inda ya bayyana wuraren da ya kasance tun bayan da aka daura auren Fatima Ganduje da Angonta Idris Ajimobi, kamar yadda Legit.ng ta gano.

KU KARANTA: Muhimmin darasi daga wata haduwa da aka yi tsakanin Sheikh Mahmud Gumi da wani Maroki

“Ranar Asabar bayan a Daura aure kamar karfe daya, na kama hanya zuwa sokoto domin bitar littafi da Sheikh Mansur ya rubuta akan sharhin iziyya, bayan nayi kwana biyu, naje Zamfara nayi wa’azi na kwana guda, daga nan na wuce Kaduna nayi program a DITV na awa biyu.” Inji Daurawa.

Sheƙe aya a bikin Fatima Ganduje: Sheikh Aminu Daurawa ya wanke kansa dangane da zargin kawar da kai

Daurawa

Shehin Malamin ya cigaba da bayanin cewa: “A ranar Juma'a na yiwa mata wa’azi a Rigasan jihar Kaduna daganan na wuce masallacin Juma’a nayi pre-kudubah kuma na gabatar da khudubar juma'a. Bayan magariba nayi waazi a masallacin Shaik Rabiu Daura.

“Ranar Asabar da safe nayiwa mata waazi a masallacin Sultan Bello. Daga nan na taho Kano.Masu son su ganni na dawo Ina office.Bayan abubuwan da suka faru a wajan bikin yar Gov kowa yana jira yaji mai Daurawa zai fada, to ku mai kuke zaton zan fada?”

Jama’a da daman a zargin hukumar ne da rashin adalci da tsoron fada ma gwamnati gaskiya duba da irin sheke ayar da aka yi a bikin Fatima Ganduje, wanda ake yi ma kallo da keta haddin musulunci da ala’adara Hausa a bikin nata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel