Mutumin Jihar Anambra ya zama babban Alkalin Kotun Duniya
Eboe-Osuji daga Najeriya ya zama babban Alkali a Kotun ICC. Osuji yayi karatun sa Digir-gir da Di-gir-di-gir a Kasar Turai. Ya kuma fara aiki da Kotun na ICC a 2007 bayan yayi aiki a Kotu ya kuma koyar a Jami’a a kasashen waje.
Wani ‘Dan Najeriya ya samu shiga cikin sahun Alkalan Duniua a wannan makon. Kotun ICC ta Duniya ta nada Chile Eboe-Osuji a matsayin Shugaban ta inda zai yi wa’adin shekaru 3. Gidan Jaridar AfricanNews ta rahoto wannan.
Alkali Eboe-Osuji wanda ‘dan Najeriya ne ya zama Shugaban Kotun ICC inda aka nada Robert Fremr na kasar Czech a matsayin Mataimakin sa na farko da kuma wani Bafaranshe Marc Perrin de Brichambaut a matsayin Mataimaki na biyu.
KU KARANTA: Wata 'Yar Boko za ta kara da Shugaba Buhari a 2019
An haifi Eboe-Osuji ne a Garin Anara da ke Jihar Anambra a 1962 kuma yayi Digirin farko ne a kan shari’a a Jani’ar Kalaba daga nan ya wuce Jami’ar Montreal ta Kanada da kuma Amsterdam ya kara karatu bayan na ya fara aiki a Kasar wajen.
Alkali Eboe-Osuji ya ji dadin wannan nadi da aka yi masa inda ya nuna cewa zai yi bakin kokarin sa da abokan aikin sa. Ministan harkokin kasar waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ya taya Alkalin murna.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng