Babban kalubale a yaki da mayakan kungiyar Boko Haram - Sojin Najeriya

Babban kalubale a yaki da mayakan kungiyar Boko Haram - Sojin Najeriya

- Wani Injiniya kuma kwamanda a hukumar sojin Najeriya ya bayyana ganowa da kwance bam a matsayin aiki mafi wahala a yaki da mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno

- Kwamandan na wannan kalamai ne a wurin wani na al'amuran walwalar al'umma kasashen Afrika ta yamma (WASA) da aka gudanar jiya Asabar a Legas

- Kwamandan soji, Manjo janar Richard Duru, ya bukaci dakarun soji da su kara jajircewa a yakin da su ke da kungiyar Boko Haram

Wani injiniya kuma kwamanda a hukumar sojin Najeriya, Manjo Janar John Amalu, ya bayyana ganowa tare da kwance bam a matsayin aiki mafi wahala a yaki da Boko Haram a jihar Borno.

"Harka da bama-bamai ya fi komai wahala a yaki da Boko Haram, kuma aikin Injiniyoyi ne ganowa tare da kwance bama-bamai," inji Amalu.

Babban kalubale a yaki da mayakan kungiyar Boko Haram - Sojin Najeriya

Sojin Najeriya

Amalu na wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi a wani taro na walwalar al'umma kasashen Afrika ta yama (WASA) jiya a Legas.

DUBA WANNAN: Ruwan bama-bamai: Al'ummar wasu kauyuka a jihar Adamawa zasu maka sojin sama a kotun ICC

Ko a cikin watannan saida wani kwamandan soji ya rasa ransa sakamakon tashin wani bam da motar da yake ciki ta taka a dajin Sambisa.

Kazalika wani kwamandan soji, Manjo Janar Richard Duru, ya jinjinawa dakarun soji tare da kara yin kira gare su da su ninka kwazon su a yakin da su ke yi da Boko Haram duk da cewar hukuma ce ke yin nasara a kan mayakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel