Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Adamawa Abubakar Saleh Michika rasuwa

Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Adamawa Abubakar Saleh Michika rasuwa

- Tsohon gwamnan jihar Adamawa Alhaji Abubakar Saleh Michika ya rasu a daren ranar Asabar

- Michika yayi gwamna a jihar Adamwa na tsawon shekara daya

Gwamna na farko a mulkin farar hula na jihar Adamawa, Alhaji Abubakar Saleh Michika, ya mutu.

Legit.ng ta samu rahoton cewa, Michika ya mutum ne a daren ranar Asabar a Cibiyar kiwon lafiya na jihar Adamawa bayan yayi fama da rashin lafiya.

Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Adamawa Abubakar Saleh Michika rasuwa
Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Adamawa Abubakar Saleh Michika rasuwa

Alhaji Abubakar Saleh Michika, ya yi gwamnan jihar Adamawa a mulkin farar hula daga shekarar 1992 zuwa 1993.

KU KARANTA : Allahu Akbar: An bude sabbin masallatai 423, an rufe coci 500 a birnin Landan

Babban yaron tsohon gwamnan, Hafiz Saleh yace, gwamnatin jihar Adamawa taki tallafa masa a lokacin da yake rashin lafiya, ya nemi su dauki nauyin tafiyar sa zuwa kasar waje dan samun kulawar kwararrun likitoci amma sun ki.

Hafiz Saleh yace, gwamnatin jihar Adamawa bata biyan sa kudin fansho din sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng