‘Dalibai 500 sun amfana da gudumuwar Sanata Abubakar Kyari a Borno
- Sanatan Yankin Borno ya taimakawa ‘Dalibai 500 da ke karatu a Jihar
- Yanzu 'Dan Majalisar na kokarin agazawa wasu ‘Dalibai 1000 a Borno
- Kusan babu wanda ya taba yin irin wannan babban aiki na Sanata Kyari
Mun samu labari cewa Sanatan Arewacin Jihar Borno Abubakar Kyari ya dauki nauyn karatun ‘Dalibai 500 da ke Makarantun da ke gaba da sakandare daga Mazabar sa. Yanzu haka ma Sanatan zai kara taimakawa wasu.
Daga cikin wadanda aka taimakawa, akwai ‘Dalibai 100 daga Jami’ar Maiduguri sai kuma wasu ‘Dalibai 400 da ke karatu a Makarantun da ke cikin Jihar Borno. Honarabul BG Galangi ya bayyana wannan a wancan makon na jiya.
KU KARANTA: Sanatoci za su yi maganin Shehu Sani na fasa masu kwai
Tsohon Shugaban tsangayar hada magunguna a Jami’ar ta Maiduguri Farfesa Isa Husseini Marte shi ne ya kaddamar da wannan abin alherin da ba a taba gani ba a Jami’ar inda ya yabawa Sanatan na taimakawa harkar ilmi.
Honarabul Babagana Galangi wanda shi ya wakilci Sanatan a taron ya bayyana cewa burin Sanata Kyari shi ne ya ga Jama’a sun yi karatun Boko. Galangi ya zayyano wasu kadan daga cikin manyan ayyukan Sanatan a wurin taron.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng