Ran Sanatoci ya baci kan bayyana kudin da suke samu da Shehu Sani yayi, sun fara shirya masa kaidi

Ran Sanatoci ya baci kan bayyana kudin da suke samu da Shehu Sani yayi, sun fara shirya masa kaidi

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani. ya batawa abokan aikinsa rai bayan ya bayyana cewa suna samun N13.5million kowani wata na ayyuka kawai banda albashin da suke samu.

Wasu sanatoci sun bayyanawa jaridar Premium Times cewa wannan fallasa da Shehu Sani yayi ya bata musu suna kuma jama'ansu ak iya juya musu baya.

Sanatocin da mambobin majalisan wakilai sunce a yanzu haka suna cikin shirya masa kaidi kuma sai sunyi maganinshi.

Ran Sanatoci ya baci kan bayyana kudin da suke samu da Shehu Sani yayi, sun fara shirya masa kaidi
Ran Sanatoci ya baci kan bayyana kudin da suke samu da Shehu Sani yayi, sun fara shirya masa kaidi
Asali: Depositphotos

Sanata Shehu ya yi hira da TheNews inda ya bayyana cewa kowani sanata na amsan N13.5 million kudin gudana, sabanin N700,000 da suke amsa kudin albashi.

KU KARANTA: Abubuwa 7 da ba lallai kun sani ba kan Yemi Osinbajo

wannan abu da ya bayyana ta tayar da hankulan yan majalisan saboda jama'an Najeriya sun fara sukansu cewa suna amsan makudan kudi kuma al'umma na cikin mawuyacin halin yunwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: