Dalibai 1, 700 za su zauna jarrabawa a jihar Borno - JAMB

Dalibai 1, 700 za su zauna jarrabawa a jihar Borno - JAMB

Mista Babagana Gutti, shugaban harkokin jarrabawa na hukumar JAMB ya bayyana cewa, kimanin dalibai masu neman shiga jami'o'i 1, 700 ne suka yi rajista da hukumar JAMB a jihar Borno.

Gutti ya bayyana hakan ne yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya, inda ya ce daliban zasu zauna jarrabawar a shiyoyi 8 na fadin jihar.

Ya bayyana cewa, kowace shiya daya da hukumar ta tanadar zata dauki kimanin dalibai 250, inda shiyoyi bakwai suke cikin birnin Maiduguri da kuma guda a garin Biu.

Dalibai 1, 700 za su zauna jarrabawa a jihar Borno - JAMB
Dalibai 1, 700 za su zauna jarrabawa a jihar Borno - JAMB

Shugaban ya kuma bayyana cewa, an cafke wasu tagwaye da laifin magudi yayin gudanar da jarrabawa a shiyar da hukumar ta tanadar ta jami'ar Maiduguri.

KARANTA KUMA: Ministan Abuja ya bayar da kyautar mota da N500, 000 ga hazikar da ta lashe gasar Al-Qur'ani

Ya kara da cewa, tagwayen sun yi amfani da dabara ta daya ya zauna a madadin daya wanda cikin rashin sa'a ma'aikatan na JAMB suka damke su.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad III, ya soki rashin tawali'u da kwalisar wasu malaman addini a fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel