Rikicin makiyaya: Obasanjo ya goyi bayan gwamna Ortom dokar kan dokar hana kiwo a jihar Benuwe

Rikicin makiyaya: Obasanjo ya goyi bayan gwamna Ortom dokar kan dokar hana kiwo a jihar Benuwe

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya goyi bayan gwamna Ortom a kan dokar hana makiyaya kiwo a jihar Benuwe

- Obasanjo ya bayyana hakan ne a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno

- Obasanjo ya ziyarci jihar Benuwe a gurguje kafin ya wuce jihar Borno

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga gwamnan jihar Benuwe a kan dokar haramtawa makiyaya kiwo a jihar.

Obasanjo ya ziyarci jihar Benuwe a gurguje a yau, Asabar, 10 ga watan Maris, 2018, kafin ya wuce jihar Borno.

Rikicin Makiyaya: Obasanjo ya goyi bayan dokar hana kiwo a jihar Benuwe
Rikicin Makiyaya: Obasanjo ya goyi bayan dokar hana kiwo a jihar Benuwe

Tsohon shugaban kasar ya karfafawa gwamna Ortom gwuiwa a kan dokar da ya kafa tun shekarar da ta gabata tare da shaida masa cewar kada ya janye dokar. Kazalika, ya ja hankalin gwamnan da ya cigaba da aiyukan da zasu inganta rayuwar mutanen jihar Benuwe.

KU KARANTA: Riginginmu shida a APC da zasu yiwa kwamitin Tinubu wahalar sulhuntawa

A yayin gajeriyar ziyarar ta sa, Obasanjo, ya ziyarci kabarin mutane 73 da makiyaya su ka hallaka ranar 1 ga watan Janairu, 2018. Obasanjo ya bayyana kisan mutanen da tsantsar rashin tausayi da ganin girman ran bil'adama.

Obasanjo ya bayyana cewar duk gwamnatin dake nufin jama'a da alheri dole ta mayar da hankali wajen kawo karshen aiyukan ta'addanci dake jawo salwantar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Bayan ya isa jihar Borno, Obasanjo, ya gudanar da wani taro domin yaki da yunwa. Wasu kungiyoyi tare da tsohon shugaban kasar ne su ka hada karfi domin yaki da karancin abinci a tsakanin talakawan Najeriya.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da wakilai daga ma'aikatar noma ta tarayya da wakilan gwamnatocin jihohin, Borno, Benuwe, Sokoto, Ogun, da Ebonyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164