Ba bu jam'iyyar PDP ba bu kayan ta a jihar Katsina - Oyegun
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana cewa, ba bu jam'iyyar PDP ba bu kayanta a jihar Katsina.
Oyegun ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani taro da jam'iyyar APC reshen jihar Katsina ta shirya domin karbar wasu manyan 'yan siyasa na jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC.
Yake cewa, a sakamakon yadda manyan 'yan siyasa da mabiyan su ke sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya tabbatar da jam'iyyun PDP, APGA da PDM ba su ba kayan su a jihar.
Shugaban jam'iyyar ya kuma kirayi al'ummar Jihar da su ci gaba da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da hakan zai kara masa karfin gwiwa na tsayuwar daka wajen jagorantar kasar nan.
KARANTA KUMA: Mutu ka raba: Sirrikan rike miji a gidan aure
A nasa jawabin gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya jinjina wa kusoshin jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC, inda yake cewa wannan ya nuna alamu na shugabanci nagari a jihar.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rayuka 4 sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya afku a garin Abuja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng