Wani masanin al'ummuran matasa ya sake janyo hankalin Buhari kan batun Peace Corps

Wani masanin al'ummuran matasa ya sake janyo hankalin Buhari kan batun Peace Corps

- Rashin amincewa da kafa Hukumar Peace Corps da shugaba Muhammadu Buhari ya yi yana kara janyo hankalin al'umma a Najeriya

- Wani masanin al'amuran matasa na kasa da kasa, Kwamared Ben Duntoye ya yi kira da shugaban kasa ya sake shawara ya amince da kudirin kafa hukumar

- Duntoye ya ce dalilan da shugaban kasa ya bayar na rashin amincewa da kudirin kafa hukumar

Wani masanni kan al'ammuran matasa kuma tsohon shugaban kungiyar hadin kan matasan nahiyar Afirka, Kwamared Ben Duntoye ya yi kira da shugaba Muhammadu Buhari ya hanzarta ya amince da kudirin kafa hukumar Peace Corps.

Direktan na Cibiyar Tallafawa Matasa Afirka, Ben Duntoye ya fadi hakan ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Maris yayin da ya kira taron manema labarai a cibiyar nasa. Ya kuma lissafo muhimman ayyukan za ta rika gudanarwa.

Wani masanin al'ummuran matasa ya sake janyo hankalin Buhari kan batun Peace Corps
Wani masanin al'ummuran matasa ya sake janyo hankalin Buhari kan batun Peace Corps

KU KARANTA: Abinda ya dace gwamnati tayi don shawo kan matsalar ta'addanci - Mama Boko Haram

Ayyukan da ya lissafo sun hada da:

1) Hada kawunnan matasa wuri guda don gudannar da ayyukan gaya da habaka al'umma.

2) Bayar da gudun mawa wajen gudanar da ayyukan kasa da suka hada da kiddiga, rajista masu zabe, gudanar da zabe da tsaftace gari.

3) Tabbatar da bin doka da Oda a makarantun gwamnati da wasu wuraren taruwan al'umma

4) Ayyukan raya al'umma

A cewarsa, Cibiyar sa ta matasa tayi nazarin kudirin na kafa Peace Corps din kafin ayi taron jin ra'ayin al'umma da majalissar tarayya tayi kuma ta gano Hukumar ta Peace Corps zai zata kasance hukumar da tafi kowacce saukin gudanarwa.

Ya kuma ce kara da cewa akwai yiwuwar wasu kasashen duniya zasu tallafa wa hukumar da kudade saboda irin ayyukan raya al'umma da zata rika gudanarwa.

Duntoye ya ce cibiyar tasa bata gamsu da dalilin da fadar shugaban kasa ta bayar ba na kin amincewa da hukumar. Ya tunnatar da shugaban kasar kan alkawarin da ya yi na samar da miliyoyin ayyuka ga matasan Najeriya inda ya ce rashin amincewa da kudirin ya ci karo da hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel