Abubuwa 7 da ba lallai kun sani ba kan Yemi Osinbajo

Abubuwa 7 da ba lallai kun sani ba kan Yemi Osinbajo

- Ka sanshi a matsayin mataimakin shugaban kasa amma iyayensa sun sanshi a Oluyemi Oluleke. A yau shekarunsa 60, kuma ba wai Uba ga iyalan gidansa kadai ba amma Uba ga miliyoyin al’ummar kasar nan

- Ya fara koyarwa a jami’a yanada shekaru 23, ya kuma ranci kudi don ya biya kudin makaranta kafin ya zama Farfesa da shekaru 33

- Bai taba hawa sabuwar mota ba sai a shekarar 1998, lokacin yana da shekaru 41, gashi har ya kai duk shekara yana samun kyautar sababbin motoci uku

Abubuwa 7 da ba lallai kun sani ba kan Yemi Osinbajo

Abubuwa 7 da ba lallai kun sani ba kan Yemi Osinbajo

Ka sanshi a matsayin mataimakin shugaban kasa amma iyayensa sun sanshi a Oluyemi Oluleke. Yau shekararsa 60, kuma ba wai Uba ga iyalin gidansa ko danginsa kadai ba amma Uba ga daukacin al’ummar kasar nan.

Duk mun sanshi a Farfesa ta fannin Shari’a, wanda fanni ne na masu kwakwalwa, amma abunda mutane daywa basu sani ba shine ya fara koyarwa yana dan shekaru 23. Ya karantar da shari’a a jami’ar Legas, inda Rilwan Akiolu Oba na Legas dalibinsa ne.

Wanda ya taba rancen kudin makaranta yau zai iya biya ma dubunnai, kila ka san cewa yayi karatu a makarantar kimiyya ta tattalin arziki da siyasa a Ingila, amma baka san cewa sai da ya ranci kudi ba sannan ya karasa karatun.

DUBA WANNAN: Ya watsa mata Acid saboda ta haifa masa mace

Wasu ‘yan shekaru baya lokacin yana karatu ya samu matsala da Bankin Najeriya na tangarda daya samu wurin turo masa kudin makaranta, inda ya samu shugaban makarantar yayi mata bayani ta shawarce shi da yaje banki ya nemi bashi na £600 wanda hakan ne ya zame masa mafita.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel