Rashin tausayi: Wani mutum a kasar Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace

Rashin tausayi: Wani mutum a kasar Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace

- Wani dan kasar India ya watsa ma matarsa guba tana bacci

- Yace yayi hakan ne saboda ta Haifa mashi diya mace bayan shi kuma namiji yakeso

- Yanzu haka Hukumar ‘Yan Sanda na nemansa ya gudu

Wani mutum mai suna Siraj mai shekaru 32, ya watsa ma matarsa mai suna Fara mai shekaru 25, guba wato acid tana cikin bacci saboda ta haifar masa diya mace shi kuma namiji yakeso.

Tayi mummunar kuna a sakamakon gubar da Siraj, wanda aka fi sani da Bhura ya zuba mata tana cikin bacci, a garin Moradabad kusa da New Delhi, a ranar Litinin kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito.

Magidanci a Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace
Magidanci a Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace

Magidanci a Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace
Magidanci a Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace

KU KARANTA: Maryam Sanda ta shirya wa diyar ta buki kwana daya bayan bayar da belin ta, ku kalli hotuna

Yace bata biyashi ladan sadakinta daya biya ba tunda bata haifa masa namiji ba. Mutumin ya ja mata munanan raunuka a jiki wanda yasa jami’an ‘yan Sanda suka shiga farautarsa.

An hanzarta kai Farah asibitin karkara sokamakon mummunan halin da ya jefata, inda ta samu kuna a Fuska, hannuwa, da kuma ciki.

Ma'aauratan dai sunyi shekara takwas tare kuma suna da yara biyu duk mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164