Maryam Sanda ta shirya wa diyar ta buki kwana daya bayan bayar da belin ta, ku kalli hotuna
Kwana daya kacal bayan babban kotun da ke Abuja ta bayar da belin Maryam Sanda, wadda ake tuhuma da laifin kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka har lahira ta shirya wa yar ta party na murnar zagayowar ranar haihuwa.
Marigayi mijin nata dan uwa ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Halliru Bello.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa taron muranar zagayowar haihuwar dai anyi shi ne ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu a gidan mahaifiyar Maryam kuma ya samu hallartan yan uwan ta na jiki.
Ga dai daya daga cikin hotunnan da aka dauka inda za'a ga Maryam ta caba ado tana rungume da yarinyar da aka shirya wa taron wato Aisha.
KU KARANTA: Mata na da kaifin basira, idan suka samu 'yanci zasu tunkude mu daga mulki - Gudaji Kazaure
A ranar Alhamis ne dai kotun ta bayar da belin Maryam bayan ta bayyana cewa tana da juna biyu kuma tana fama da rashin lafiya.
Joseph Daudu, lauya mai kare Maryam Sanda ya roki kotu ta tausaya wa Maryam domin halin da take ciki saboda ta je asibiti ta samu kulawa mai kyau.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng