Muhimmin darasi daga wata haduwa da aka yi tsakanin Sheikh Mahmud Gumi da wani Maroki

Muhimmin darasi daga wata haduwa da aka yi tsakanin Sheikh Mahmud Gumi da wani Maroki

A yau Legit.ng ta kalato muku wani labara da ya faru a tsakanin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ya gabata, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da wani maroki, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Wata rana ne wani maroki mai tsananin hikima ya niki gari, yayi takanas takano zuwa gidan sheikh Gumi dake cikin garin Kaduna don ya gana da shi, inda ya isa gidan da misalin karfe na 11 na safe.

KU KARANTA: Daga jin Mijinta zai kara aure, Matarsa ta banka ma gidansa wuta a Kebbi

Da isarsa sai ya tarar da almajiran Malam na zaune a waje, inda ya bukaci ayi masa sallama da Malam, su kuma suka ce a’a don kwua Malam baya tashi barci a yanzu, kuma ba zai fito ba sai lokacin sallar Azahar.

Muhimmin darasi daga wata haduwa da aka yi tsakanin Sheikh Mahmud Gumi da wani Maroki
Sheikh Mahmud Gumi

Wannan maroki ya yi musu magiya don ganin sun yi masa sallama da Malam amma abin ya ci tura, hakan ya tunzura shi, yace musu ‘Bari kuga yanzu zai fito”, nan da nan ya tafi saitin tagar dakin Malam, inda ya fara kwala kiran Sallah, har zuwa karshe.

Kafin kace me, sai ga Malam ya fito, inda ya tambayi almajiransa menene dalilin kiran Sallah a yanzu alhali lokacinta bai yi ba? Sai suka nuna ma Malam wannan maroki dake neman ganinsa cikin ujila.

“Ni na kira Sallah Malam, na yi ne don ina son ganinka, kuma an ce min ba zaka fito ba sai lokacin sallar Azahar”, “Meke tafe da kai?” Inji Malam, sai marokin ya fada ma Malam cewar yazo maula ne, hakan ya daure ma Malam kai, inda yace masa: “Yanzu maular taku har ta kai ga Malama.?”

Abinka da sarkin Maroka, sai marokin nan ya kada baki yace da Malam: “Ai su suka fi dacewa a yi ma maula, saboda sune suka karanta ayar da ta hana bara, kuma sune suka san falalar bada sadaka.”

Nan fa Malam yayi murmushi, ya shiga cikin gida ya aro kudi a wajen iyalinsa, ya baiwa wannan bawan Allah, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng