Mata na da kaifin basira, idan suka samu 'yanci zasu tunkude mu daga mulki - Gudaji Kazaure
- Wani dan majalisa ya gargadi sauran abokan aikin sa da kw majalisar Wakilai na Tarayya
- Dan majalisan yace mata suna da basira sosai kuma idan aka basu yanci da yawa zasu hambare maza
- Gudaji Kazaure ya yi wannan furuci ne a jawabin sa na yayin da Majalisar ta bada filin don tsokaci kan ranar mata na duniya
Dan Majalisan Dattawa Gudaji Muhammad Kazaure ya gargadi sauran abokan aikin sa na Majalisar kan bawa mata yanci da daura su kan karagar mulki Najeriya.
Dan Majalisar mai wakiltan yankunnan Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankawashi na jihar Jigawa ya ce duk lokacin da aka bawa mata yanci da yawa, sukan kwace mulkin ne gaba daya daga hannun mazan saboda kaifin basirar su.
A jawabin sa na muranar ranar mata na duniya, Kazaure ya ce "Yana da kyau a karfafa wa mata gwiwa a harkar siyasa da kasuwanci saboda irin rawar da suke takawa a rayuwar mu.
KU KARANTA: Abu daya da gwamnati za tayi don kawo karshen Boko Haram - Obasanjo
"Amma abin da nake tsoro shine matan fa sune ke mulkar mazajen su a gida, idan aka basu yanci sosai a waje, za su mamaye ko ina.
"Idan aka basu yanci sosai, wata rana zasu hambare mazar. Muna iya zuwa Majalisar mu tarar muta sun mamaye ko ina kuma abubuwa ba za su tafi daidai ba saboda suna da basira sosai," inji shi.
Kazaure ya yi wannan jawabin ne a ranar da aka ware don murnar zagayowar mata na duniya.
A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa wani Dan Majalisa mai wakiltar Dustsinma/Kurfi ya tallafa wa mata 2000 da jarin don fara sana'o'i da zasu rike kansu.
Danlami kurfi ya ce tallafin da ya bawa matan ya lashe kudi naira miliyan 30 kuma an rabar ne ga mata daga garuruwan da ke karkashin yankunan da yake wakilta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng