Tsautsayi: Jirgin kasa ya murkushe Baiwar Allah mai yi wa kasa hidima a Legas
- An wayi Legas da takaici bayan an rasa Budurwar da ke aikin NYSC
- Wata Budurwa ta rasu bayan tayi mugun hadari a titin jirgin kasa
- Wannan Baiwar Allah tana yi wa kasa hidima ne a cikin Garin Ikeja
Mun samu labari mai ban tausayi na wata Budurwa da jirgin kasa yayi kuli-kulin kubura da ita bayan ta toshe kunnuwan ta tana tafiya a kan mahadar jirgin kasar a Garin Ikeja.
Wannan Baiwar Allah mai aikin NYSC gamu da ajalin ta ne bayan ta sanya na’urar jin sauti a cikin kunnuwan ta a kan titin jirgi. Wannan Baiwar Allah ta karya yatsu 3 bayan kuma karaya iri-iri da ta samu har daga baya ta cika.
KU KARANTA: An rufe coci an bude Masallatai a Birnin Landan
Jaridar DAILY INDEPENDENT ta rahoto cewa Mohammed Momoh wanda shi ne Jami’in NYSC na Jihar Legas sanar da cewa wannan Budurwa ta rasu a asibitin koyarwa ta Jami’ar Legas yayin da ake duba ta inda ya jajantawa jama’a.
Hukumar NYSC ta yabawa Shugaban Karamar Hukumar Ikeja Mojeed Alabi Balogun wanda ya biya kudin maganin Baiwar Allah a asibiti. Ba mamaki mamaciyar ta sa kida ne a kunnuwan ta har jirgin yayi ta kara amma ba ta ji ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng