An kama wani Sojan sama na karya da ke yaudarar Jama'a

An kama wani Sojan sama na karya da ke yaudarar Jama'a

- Wani Sojan karya ya shiga hannun Jami'an tsaro a Garin Katsina

- Nasir Abu yana damfarar Jama'a da sunan cewa Sojan sama ne shi

- An gano cewa an taba korar wannan mutumi daga gidan Soja a baya

Mun samu labari daga gidan kuratan Sojojin Najeriya da ke Zaria a cikin Jihar Kaduna cewa an kama wani mai suna Nasir Abu sanye da kayan Sojoji inda yake damfarar Jama'a a matsayin Sojan saman Najeriya.

An kama wani Sojan sama na karya da ke yaudarar Jama'a
Jami'an tsaro sun damke wani Sojan bogi

An damke Nasir Abu mai shekaru 34 ne a Ramin Kura kusa da filin folo a cikin Garin Katsina. Wannan Bawan Allah yayi abin da ya saba kenan da damfarar wata Baiwar Allah Saudatu Muhammed Bugaje a Unguwar Kofar Kaura da ke cikin Katsina.

KU KARANTA:

Wannan Bawan Allah ya karbe wata shamfadediyar waya kirar Techno K7 ya kusan N33,000 da kuma kudi. Ya kuma karbewa wannan mata zoben ta na gwal. Bayan nan ya karbi buhunan shinkafa daga wani dan kasuwa mai suna Jariri Dando.

A binciken da aka gudanar an samu wannan mutumi da kayan Sojojin sama da huluna har sa baje da igiya. An kuma same shi dauke da layin waya sama da 10 da kuma mota kirar Golf III wagon. Tuni dai ya amsa laifin sa. An dai ma taba korar sa daga aikin Soja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng