Ta mallakawa Karyarta dukiyarta duka ta bar dan cikinta yana yawon dandi
- Abin al'ajabi baya karewa a duniyar nan, duk dai wannan bashi ne na farko ba an sha yin hakan
- Wata mata a kasar Amurka ta mallakawa wata karya duka dukiyar ta bar danta na cikin ta yana yawon dandi
-Matar wacce take hamshakiyar mai kudi ce ta bada wasiyar bawa karyar dukiyar ta bayan rasuwar ta
Wata mata data rasu a kasar Amurka ta mallakawa karyar ta kudi dala milyan 30 da gidaje, inda ta mallakawa danta na cikinta dala miliyan daya kacal.
Matar mai shekaru 67 mai suna, Gail Posner, ta rasu ta bar dukiya mai yawa da gidaje manya a birnin Florida da Miami, matar ta dankawa ma'aikatan gidan nata dukiyar ta da kudi masu dinbin yawa, wanda zai ishe su kula da dukkan bukatun karyar har karshen rayuwarta.
DUBA WANNAN: To fa: Trump zai gana da shugaban Koriya ta Arewa a watan Mayu
Karyar mai suna Chihuahua wacce ta mallaki mota kirar kamfanin Limousine, da wani makeken gida mai dauke da dakuna guda 7, tana nan zaune abinta bata da aiki sai dai ta ci abinci wanda wata mai aikin abincin gidan ke dafa mata mai dan karen dadi.
Lamarin mai ban mamaki wanda ya ke ciwa yaron marigayiyar mai suna Bret Carr tuwo a kwarya, ya kasa daurewa ya nufi kotu a fusace, don a tabbatar masa da shin kuwa mahaifiyar tasa tana cikin hankalinta ta aikata wannan abin, ko kuwa ma'aikatan tane suka hada wata makarkashiyar su, don su cinye dukiyar mahaifiyar tashi.
Wasu mutane wanda suka san matar sosai sun ce:
"Abinda ta yi din ba abin mamaki bane domin kuwa tun lokacin da tana da rai, tana almubazzaranci yanda ranta yake so, to dan ta bawa karya dukiyar ta hakan ba zai daure musu kai ba."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng