Inyamurai na cikin hadarin fama da cutar makanta a Najeriya
- Bincike ya nuna cewa mafi yawan masu cutar glaucoma Inyamurai ne
- Kuma masu fama da cutar hawan jini da Gwauraye na yawan kamuwa
- Akwai sama da mutane Miliyan 64 a Duniya da ke dauke da Glaucoma
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa mutanen Kabilar Inyamurai su na cikin hadarin daukar cutar makanta ta glaucoma. Haka ma Gwauraye da Tuzurai musamman maza na iya kamuwa da wannan mugun cuta.
Bincike ya nuna cewa cutar na da nasaba da Kabilar mutum kuma Inyamurai da Yarbawa sun fi shiga cikin wanna matsala. Haka kuma maza sun fi mata yiwuwar kamuwa da cutar kamar yadda Kungiyar da ke binciken makafi a Najeriya ta bayyana.
KU KARANTA: Dan Najeriya ya kirkiro maganin cutar makanta a Duniya
Sauran kabilu irin Urhobo da da Kanuri sa kuna Hausawa ba su cika kamuwa da cutar ba. Haka kuma nazarin da aka yi ya nuna cewa jahilai sun fi saukin kamuwa da cutar. Cutar hawan jini kuma na cikin abubuwan da ke tunzura cutar ta makanta.
A shekarar 2013 akwai sama da mutane Miliyan 64 da ke dama da cutar wanda mafi yawanci tsofaffi ne. Ana sa rai nan sa shekaru 2 masu fama fa cutar sai sun karu da sama da mutum Miliyan 10.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng