Ziyarar Shugaba Buhari jihar Rivers baza ta saka matacciyar jam'iyyar APC ta tashi jihar ba - Wike
- An dade ana samun rabuwan kan siyasa a kasar nan, inda zaka ji wannan jam'iyyar da wannan jam'iyyar ba bu hadin kai a tsakanin su duk kuwa da cewa kasa daya ake al'umma daya
- Rashin jituwar yayi tsamari ne tun lokacin da jam'iyyar APC ta kwace mulki daga hannun jam'iyyar PDP wacce tayi shekaru goma sha shida tana mulki
- A kwanan nan ne ake sa ran shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Rivers, yankin kudancin kasar nan, to sai dai kamar gwamnatin jihar bata maraba da ziyarar ta sh

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari zai kawo jihar ta na da alaka da taso da matacciyar jam'iyyar APC a jihar.
Ya ce: "Na ji an ce shugaban kasa zai zo jihar mu, amma babu wanda ya sanar dani zai zo, kuma ba a fada mini dalilin zuwan nashi ba. Yana da ikon zuwa kowacce jiha a kasar nan, amma mu bamu san dalilin zuwan nashi jihar tamu ba.
DUBA WANNAN: Musulmai za su mulki duniya, idan har suka rungumi Alkur'ani hannu biyu - Inji wani Fasto a kasar Rasha
"Ina jin shugaban kasar zai zo ne domin ya taso da matacciyar jam'iyyar su ta APC da ta jima da mutuwa a jihar nan, in ji shi.
"Mu a iya sanin mu banda Yesu Almasihu, babu wanda muka san yana tada abinda ya mutu. APC ta riga ta mutu a jihar Rivers, kuma babu wani abu da zaku iya yi wanda zai dawo da ita.
"Sannan ina mai tabbatar muku da cewa kada kowa ya damu kanshi da zuwan shugaban kasar, akan matsalar tsaro. Saboda mu bamu da matsalar tsaro a jihar mu.
Ba mu taba samun matsalar makiyaya ba a jihar mu. Sannan ya kara da cewa babu wata jiha a kasar nan da babu masu garkuwa da mutane ko 'yan fashi. Ya ce idan har shugaban kasar zai zo saboda sune to sai dai ya zagaya kowacce jiha a kasar nan, domin suna kowacce jiha.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng