Yan KAROTA sun ci na jaki a hannu direbobin A daidaita sahu a sakamakon wani hatsari da suka ja
An baiwa hammata iska a tsakanin jami’an hukumar jaddada dokokin tuki a jihar Kano, KAROTA, da direbobin a daidaita sahu a daidai shatalelen dangi, inji rahaton jaridar Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Maris, a lokacin da wani jami’in KAROTA ya yi kokarin kama wani direban A daidaita sahu da ya dauki fasinja a kujerar gaba, wanda hakan ya saba ma dokar tuki a jihar Kano.
KU KARANTA: Kishi kumallon mata: Uwargida ta hallaka Mijinta da hanyar sheme shi da tabarya a jihar Neja
Sai dai da yake kafin dan KAROTA yazo, direban ya tsere, amma sai da jami’in ya bishi a sukuwane, inda yayi kokarin juya kan a daidaitan, wanda hakan yayi sanadiyyar faduwarta, inda direban tare da fasinjansa guda suka jikkata.
Wani shaidan gani da ido mai suna Haidar Abdullahi yace ganin haka ya sa sauran direbobin A daidaita sahu suka diran ma wannan jami’in KAROTA, inda suka lallasa shi, yayin da sauran yan KAROTAn suka ranta ana kare, sa’annan suka tare hanyar don bukatar a biya dan uwansu diyyar asarar da yayi.
Wani daga cikin direbobin yace: “Mun gaji da akar wahalar da muke sha a hannun jami’an KAROTA da yansandan MTD, a baya muna biyan N100 a kullum a matsayin haraji, amma da yake zabe ya karato, sun dakatar da karbar harajin, don haka yasa suke wulakanta mu.”
Dayake tattaunawa da manema labaru, shugaban hukumar KAROTA, Ibrahim Garba Kabara yace direban a daidaita sahun ne ya janyo hatsarin a lokacin da yayi nufin tserewa don kada a kama shi. Sa’annan yayi kira ga direbobin a daidaita sahu su dinga bin dokokin tuki.
Shima Kaakakin rundunar Yasnandan jihar, SP Magaji Musa Majiya yace: “Mun aika da jami’an mu don shawo kan lamarin, yayin da muka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Murtala, kuma mun kama jami’an KAROTAn da suka aikata hakan, zasu fuskanci hukunci.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng