Sirrika 7 da ya kamata kowane Musulmi ya sani akan ruwan Zam-Zam

Sirrika 7 da ya kamata kowane Musulmi ya sani akan ruwan Zam-Zam

Da sanadin shafin yanar gizo na lifeinsaudiarabia.net, Legit.ng ta kawo muku wasu sirrika goma da ruwan Zam-Zam ya kunsa da kuma ya dace a ce kowane musulmi ya ribaci ilimin da suke tafe da shi domin yada shi ga sauran al'umma.

Ruwan Zam-Zam
Ruwan Zam-Zam

1. Asalin Ruwan Zam-Zam: Dan Hajara Annabi Isma'il, tsira da aminci su kara tabbata a gare su, ya tsunduma cikin yunwa da kishirwa bayan guzuri ya yanke da mahaifin sa Annabi Ibrahim ya bari.

A sakamakon tausayi da jin kai irin na uwa ga dan ta, ta shiga kai komo tare da hawa da sauka a kan duwatsun Safa da Marwa wajen neman abin da dan ta zai sanya a baka. Bayan wannan kai komo har sau bakwai sai kawai cikin mamaki ta ankare da wani ruwa dake gudana a karkashin inda sawayen dan ta, Annabi Isma'il.

2. Wasu sunaye da ake yiwa ruwan lakabi: Akan kirayi ruwan Zam-Zam da Maimoona, Shabbaa'a da kuma Murwiya.

3. Karfin jiki: Binciken wani masanin kimiyya na kasar Jamus, Dakta Knut Pfeiffer ya bayyana cewa, kwayoyin halittu na jikin dan Adam su kan zabura da zarar an kwankwadi ruwan Zam-Zam.

KARANTA KUMA: Yajin Aiki ya janyo rabuwar kawunan Ma'aikata a Jami'ar Ahmadu Bello

4. Amfani: Alfanun ruwan Zam-Zam ba su da iyaka, ya kan biya bukata duk wata niyya da aka sha ruwan domin ta.

5. Kiwon Lafiya: Ruwan Zam-Zam ya kunshi sunadaran Magnesium da Calcium dake kawar da wata cuta mai kwazaba.

6. Tarihi: Tun shekaru sama da 4000 da suka gabata, ruwan Zam-Zam yake ta gudana ba bu kakkautawa.

7. Tsafta: Bincike ya bayyana cewa ba bu wani tsaftaceccen ruwa da zai goga kafada da ruwan Zam-Zam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng