Wata sabuwar kungiya ta fito domin sharewa Almajirai hawaye a jihar Kaduna
- Matsalar almajirai babbar baraza ce dai a Najeriya musamman ma arewacin kasar
- Hukumomi da yawa sun fito suna neman hanyar da za abi domin kawo gyara a tsarin almajiranci a kasar amma abin yaci tura
- Ana haka sai ga wata sabuwar kungiya ta fito a Kaduna mai suna Brighter Brains, domin sharewa almajiran hawayen su
Almajirai yara ne a arewacin Najeriya wanda talauci yake tilasta iyayensu bada su ga wasu malaman addini domin karatu. Almajirai suna yawo lungu-lungu, gida gida da wuraren sai da abinci domin su samu wanda zai basu guntun wanda aka ci aka rage, wasu ma har shara suke bi domin su samu abinda zasu saka a bakin salatin su.
DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC bata da wani tsari na son kawo cigaba ga matasa - Dino Melaye
Wata sabuwar kungiya a cikin garin Kaduna mai suna Brighter Brains Institute, ta fito da wata sabuwar hanya da zata sharewa almajiran hawaye, inda zata ke raba musu abinci kamar irinsu shinkafa, nama, da dai sauransu.
Kwanakin baya ma kungiyar ta yi kokarin tallafawa kusan a kalla yara 50 da abinci, inda sanadiyyar haka yasa da yawa daga cikin almajiran basu fita yawon baran da suka saba ba a cikin garin Kadunan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng