Rikicin kasuwan magani: Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 63 a kotu
- Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 63 a kotu akan rikicin kasuwar magani
- Rikicin kasuwan magani yayi sanadiyar mutuwar mutane 12 da asarar dukiyoyi
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umurci jami’an tsaron jihar da su taso masa keyar wadanda suka tada rikicin Kasuwar Magani dake Kajuru, jihar Kaduna.
A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai, ya umarci jami’an tsaron jihar, da su taso masa keyar mutanen da suka haddasa rikicin da aka yi a Kasuwar Magani wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 12 da asarar dukiyoyi masu dimbin yawa.
Gwamnatin jihar Kaduna ta maka mutane 63 a kotu wadanda akae zargi suna da hanni dumu-duma wajen ta da rikicin.
KU KARANTA : Hukumar lekan asiri ta NIA suna farautar wani Jakadan Najeriya
Babban Sakataren ma’aikatan shari’a na jihar,Kaduna, Mitsa Chris Umaru, ya bayyana haka a ranar Laraba a lokacin da ya zanta da manema labaru a birnin Kaduna.
Bayan haka kotun ta daga zaman ta zuwa ranar 15 ga watan Maris domin ci gaba da shari’ar, sannan ta bada umurnin a ci gaba da daure mutanen kurkuku zuwa wannan rana.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng