Rikicin Siyasar Kano: APC zata iya korar Kwankwaso daga jam'iyyar bisa watsi da yayi da katin gayyatar bikin 'yar gidan Ganduje

Rikicin Siyasar Kano: APC zata iya korar Kwankwaso daga jam'iyyar bisa watsi da yayi da katin gayyatar bikin 'yar gidan Ganduje

- Har yanzu dai rikici9n siyasar jihar Kano ya ki karewa inda jam'iyyar APC take ta faman kokari domin ganin ta sasanta rikicin, amma abin ya ci tura

- A satin daya gabata ne aka yi bikin yar gidan Ganduje da dan gidan Gwamnan Oyo, wanda manyan shugabannin kasar nan suka halarta ciki kuwa hadda shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shine ya zama waliyyin ango

- Sai dai kuma har aka yi bikin aka gama ba a ga keyar Sanatan Kano ta tsakiya ba wato Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, inda mutane da yawa suke ganin kamar hakan yana da nasaba da rikicin da ke tsakanin Gwamnan Kanon da Sanatan

Rikicin Siyasar Kano: APC zata iya korar Kwankwaso daga jam'iyyar bisa watsi da yayi da katin gayyatar bikin 'yar gidan Ganduje

Rikicin Siyasar Kano: APC zata iya korar Kwankwaso daga jam'iyyar bisa watsi da yayi da katin gayyatar bikin 'yar gidan Ganduje

Kwamishinan raya birni da karkara na Jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce dan majalisar mai wakiltar Kano ta tsakiya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, kila ya jawowa kansa kora da ga jam’iyar ta APC, sakamakon watsi da ya yi da kiran da kungiyar tayi ma shi wadda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta.

DUBA WANNAN: Trump yana neman sake jefa duniya cikin rikici

Iliyasu Kwankwaso ya ce jam’iyar za ta zama ba tsari idan har ba a hukunta Dan Majalisar ba, musamman na kin amsa kiran Shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan jam’iya. Kwamishinan wanda dan uwa ne ga Dan Majalisar, ya fadawa manema labarai a jiya cewa, kungiyar karkashin jagorancin Bola Tinubu ta gayyaci Kwankwaso zuwa bikin 'yar Gwamnan jihar Ganduje don sasanta tsakanin su, amma dan majalisar ya zabi yin watsin da gayyar wanda hakan ke nuna bai shirya sasantawar ba.

Kwamishinan ya kara da cewa wannan rashin daraja kiran da akayi ma sa da kuma halayyar da ya ke nunawa na nufin ya bar jam’iyar mu ta APC, da ma tuni ya zabi ya bi ‘yan Kungiyar Obasanjo. An gayyace shi bikin ne musamman dan a daidaita tsakanin sa da Gwamnan amma yaki zuwa, wanda hakan ya sa ina mai tabbatar muku da cewar ya na hanyar barin ‘jam’iyar.

Iliyasu Kwankwaso ya ce ko Sanatan da abokan tafiyar sa na so ko basa so Ganduje da Buhari ba wai takara kadai zasu tsaya ba, sai sun ci zaben 2019.

Ya ce, ba wai ra’ayin Buhari na tsayawa takara ko kin tsayawa ba, magana ce ta abun da jam’iya da mutanen Najeriya suka riga suka yanke hukunci a kai tuntuni, saboda sun riga sun bashi hadin kai da goyon baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel