Birtaniya zata gina gidan yari a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta ware dala miliyan daya dan shirya gina wani bangaren gidan kaso a Najeriya
- Gidan kason da Britaniya zata gina a Najeriya zai dauki gadaje guda 112
Gwamnatin Birtaniya ta fara shirin kashe dala miliyan daya wajen gina gina sabon bangaren gidan kaso a Najeriya.
Sakataren harkan kasashen waje na kasar Birtaniya, Mista Boris Johnson, wanda ya sanar da haka, ya ce akwai yarjejeniyar sauyin gidan kaso na dole tsakanin kasashen biyu.
Yarjejeniyar za ta baiwa wasu fursunoni da su ka cancanta damar a dawo da su domin karasa hukuncinsu a kasashen su.
KU KARANTA : Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai
Britaniya zata yi aikin ginin ne a gidan yari na Kiri-Kiri dake jihar Legas wanda zai dauki gadaje guda 112.
A shekarar da ta gabata ne shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari ya bayar da umarnin rage cunkoso a gidajen kason kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng