Kishi kumallon mata: Uwargida ta hallaka Mijinta da hanyar sheme shi da tabarya a jihar Neja

Kishi kumallon mata: Uwargida ta hallaka Mijinta da hanyar sheme shi da tabarya a jihar Neja

Jami’an hukumar Yansandan Najeriya reshen jihar Neja sun yi caraf da wata Mata da ta kashe mijinta ta hanyar zabga masa tabarya a kai, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Maris, inda tsananin kishi ya kwashi matar mai suna Hajiya Balaraba ta jibga ma Mijinta mai suna Malam Sani Doctor tabarya a kai, inda yace ga garinku nan bayan haka.

KU KARANTA: Tafiyayye ne: An karrama wani Malami dake shafe kilomita 42 a ƙasa a kullum don zuwa makaranta

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Kasanga dake cikin karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja, kamar yadda majiyar ta tabbatar, wani mazaunin garin mai suna Nura Alhasan ya bayyana musabbabib kisan Sani Doctor da Balaraba ta yi.

“Tsananin kishi ne ya kwasheta har ta tafka wannan aika aika, saboda Malam Sani na auren mata uku ne, inda ya hada guda biyu a gida daya, yayin da Balaraba wanda itace uwargida take zaune ita kadai, zuwan da ya yi wajen matan nasa guda biyu ne ya harzuka Balaraba, wanda a ranar daya dawo ta fara zarginsa da cewa ya wulakanta ta.

“Daga nan fa sai ma’auratan suka fara cacar baki, suna musayar yawu da juna, cikin fushi uwargida Balaraba ta dauki tabarya ta dankara ma Sani Dakta a kai, tsananin bugun ya sa nan take ya fadi matacce.” Inji Malam Nura.

Sai dai shaidan yace ganin hakan ya sanya Balarab garzayawa gidan Sarkin garin, inda ta bayyana masa abinda ta yi, shi kuma ya mika ta hannun Yansanda don gudanar da bincike.

Majiyar ya tabbatar da cewa ko a kwanakin baya, sai da Sani ya saki Balaraba, amma kuma daga bisani suka sulhunta kansu, sa’annan ya mayar da ita gidansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: