Ba’a bar zamanin juyin mulki ba – Ekweremadu yayi gargadi

Ba’a bar zamanin juyin mulki ba – Ekweremadu yayi gargadi

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya ce damokradiyar kasar na ja da baya sannan kuma ba aibu bane don sojoji sunyi juyin mulki.

Ekweremadu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayinda yake bayar da gudunmawarsa a wani fafatawa da sanatan dake wakiltan Kogi ta tsakiya Ahmed Ogembe ya shirya.

Ogembe yayi zargin cewa Yahaya Bello, Gwamnan jihar Kogi, ya yi hayan yan iska domin su hargitsa wani shirin tallafi day a shirya a mazabarsa.

Mataimakin shugaban majalisar wakilan yace irin wannan lamari ya nuna cewa dole ayi kokari domin ganin an kare damokradiyar kasar.

Ba’a bar zamanin juyin mulki ba – Ekweremadu yayi gargadi

Ba’a bar zamanin juyin mulki ba – Ekweremadu yayi gargadi

Ya kawo misalai daban-daban na inda aka ci zarafin yan majalisar tarayya, inda yayi gargadin cewa kada a kuskura ayi wasa da damokradiyar kasar.

KU KARANTA KUMA: Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai

Ekweremadu ya kuma fada ma gwamnan jihar Kogi cewa hanyar day a dauka ba mai billewa bane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel