Tsohon najadu: An kama dan shekaru 63 dake garkuwa da mutane, an samu motocci 35 tare da shi

Tsohon najadu: An kama dan shekaru 63 dake garkuwa da mutane, an samu motocci 35 tare da shi

- Wani gawurtacen mai garkuwa da mutane wanda ya dade yana dabar al'umma ya shiga hannun hukuma a jihar Neja

- An kama Maitarari Isa Saidu dan shekara 63 ne tare da wasu mutane 48 ciki ma har da yayan cikin sa guda biyu

- Maitarari ya bayyana cewa yana da hannu cikin satar mutane a jihohin Arewa da dama amma daga baya ya koma siya da sayar da motoccin sata

A ranar Laraba ne Hukumar Yan sandan Najeriya ta gabatar wa manema labarai wani tsohon gawurtacen mai garkuwa da mutane, Maitarari Isa Saidu wanda aka kama shi tare da motoccin sata guda 35.

Mai magana da yawun Hukumar Yan sanda, Jimoh Moshood ne ya gabatar da shi a garin Minna tare da wasu mutane 48 da ake tuhuma ciki har da yaran cikin sa guda biyu.

Yan sanda sun kama wani gawurtacen barawo da motoccin sata 35 a jihar Neja
Yan sanda sun kama wani gawurtacen barawo da motoccin sata 35 a jihar Neja

Tsohon mai shekaru 63, yara 29 da mata uku, ya bayyana wa manema labarai cewa yana da hannu cikin satan mutane da aka rika yi a jihohin Zamfara, Kaduna, Abuja, Yobe da ma sauran jihohin Arewa maso Gabashin kasar nan.

DUBA WANNAN: Ta sharara wa malamar makaranta mari, an tisa keyar ta zuwa gidan yari

Ya ce ya karbi N300m da kuma N170m daga iyalan wadanda ya sace kafin nan ya mayar da hankali wajen siyan motoccin sata. Ya cigaba da cewa Yan sanda sun gano motoccin sata 28 a gidajen ajiyar sa na Neja da Abuja sai kuma wasu motoccin 15 daga Zamfara da ma wasu daga Kaduna.

A cewarsa "A cewarsa, garkuwa da mutane yana da hatsari sosai shi yasa ya koma siyan motoccin sata kuma ya dan dauki lokaci cikin harkar."

Ya ce dubun sa ya cika ne bayan yaran sa sun siyo wata mota a N400,000, shi kuma ya karba don ya sayar da motar kan kudi N800,000 a Kano amma sai jami'an Yan sanda sukayi ram da shi.

A yayin gabatar da su ga manema labaran, Jimoh Moshood ya ce an same su da bindigogi kirar AK47 kuma za'a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kamalla bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel