Akwai Yunwa Haram a wannan gwamnatin - Sule Lamido

Akwai Yunwa Haram a wannan gwamnatin - Sule Lamido

- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya dira a jihar Kuros Riba domin neman goyon bayan 'ya'yan jam'iyyar PDP

- Ya soki gwamnatin shugaba Buhari da hawa mulki babu kwakwkwaran shiri baya ga rashin basira

- Ya ce yanzu a Najeriya akwai Yunwa Haram bayan Boko Haram

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma mai neman jam'iyyar PDP ta tsayar da shi takara, Alhaji Sule Lamido, ya soki gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari da rashin basira.

Lamido ya zargi gwamnatin da rashin kyakykyawar manufar da zata ci da kasar nan gaba.

Akwai Yunwa Haram a wannan gwamnatin - Sule Lamido
Sule Lamido
Asali: UGC

Lamido na wadannan kalamai ne a jihar Kuros Riba domin neman goyon bayan 'ya'yan jam'iyyar PDP a zaben fitar da dantakara da jam'iyyar zata gudanar kafin babban zaben 2019.

DUBA WANNAN: Ganduje ya ware miliyan N26m domin bikin ranar mata ta duniya

Da yake jawabi yayin da ya ziyarci gwamnan jihar, Ben Ayade, Lamido, ya ce jam'iyyar PDP ce ta san mutunci da kimar 'yan Najeriya kuma take gudanar da mulki ba tare da nuna wariya ga kowacce kabila ko addini ba.

"A yau muna fama da gurguncewar gwamnati saboda sun karbi mulki ba tare da wani shiri ba. Sun hada kai ne kawai domin karbar mulki amma ba don kishin jama'a na. Shi yasa yanzu mu ke fama da Yunwa Haram," inji Lamido.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: