Ganduje ya ware miliyan N26m domin bikin ranar mata ta duniya
- Gwamnatin jihar Kano ta ware miliyan N26m domin bikin ranar mata ta duniya
- Kwamishinar mata a jihar Kano, Hajiya 'Yar-dada Bichi ta sanar da hakan ga manema labarai yayin ganawa da manema labarai
- 'Yar-dada ta ce gwamnatin jihar zata karrama wasu mata 10 a ranar, gobe, 8 ga watan Maris
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware zunzurutun kudi har miliyan N26m domin bikin ranar mata ta duniya. Gwamnatin ta ce ta ware kudin ne domin tallafawa mata a jihar.
Kwamishinar mata a jihar, Hajiya 'Yar-dada Maikano Bichi, ta sanar da haka ga manema labarai tare da bayyana cewar bikin zai samu halartar mata 2,000 daga fadin kananan hukumomin jihar 44. Ta ce za a faro shagalin bikin ne daga karamar hukumar Tudun Wada.
Kazalika ta bayyana cewar an zabi mata 1,000 domin ba su tallafin jarin kudi da zasu fara sana'o'in dogaro da kai.
DUBA WANNAN: Kotun Najeriya ta fitar da sabbin ka'idojin a kan tallar kwaroron roba
'Yar-dada ta kara da cewar majalisar dinkin duniya ce ta kirkiri ranar 10 ga watan Maris na kowacce shekara domin yabawa gwarazan mata da su ka bayar da gudunmawa a bangarorin rayuwa daban-daban.
An fara bikin ne tun shekarar 1910.
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata karrama wasu mata 10 yayin bikin da za a gudanar gobe, Alhamis, 8 ga watan Maris.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng