Tsohon ma’aikacin diflomasiyya, Mamman Daura ya rasu
Allah ya yi wa tsohon ma’aikacin diflomasiyya sannan kuma tsohon darakta Janar na hukumar Technical Aid Corps, Mamman Daura rasuwa.
Marigayin ya rasu ne yana da shekaru 71 a duniya.
A cewar majiya daga yan uwan marigayin, ya rasu ne a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu da misalin karfe 7 na yamma a gidansa dake Aso Drive Abuja bayan dan gajeren rashin lafiya.
Marigayi Daura yayi aiki a matsayin jakadan Najeriya a kasar Uganda na tsawon shekaru takwas.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Layikan mai sun gurgunta al’amura a Kaduna yayinda Buhari zai ziyarci jihar
Ya kuma yi aiki a kasar Saudiyya, Korea ta Kudu, Belgium da kuma kasar Kamaru.
Za a binne shi a yau a garin Daura kamar yadda addinin Islama ta koyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng