Allah ya kiyaye, Saura kiris sabuwar rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa a Ile-Ife
Shekara daya bayan rikicin da akayi asaran rayuka a garin Ile-Ife jihar Osun, saura kiris sabuwar rikici ya barke tsakanin yan kabilar Yoruba da Hausawa su yi sabuwar rikicin amma da alamun shugabanni sun kawar.
Rahoton da muka samu daga Daily Trust cewa an samu labarin cewa wasu Hausawa sun iso garin Ile-Ife domin cin rani amma lokacin da mazauna Ile-Ife suka ga haka, sai hankalinsu ya tashi.
Da wannan labari ya isa fadar sarkin Yarabawa, Ooni of Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya aika manyan fadawansa su dakile wannan tashin hankali amma da alamun sun gaza.
Rahoton ya bayyana cewa fadawan sun gayyaci sakin Hausawan Sabo Ile-Ife, Alhaji Mahmoud Madagali, domin rattaba hannu kan wasu takardu kafin a amince Hausawan su zauna a garin amma sai Sarkin Hausawa ya ki, da hujjan cewa ai yan Najeriya ne kuma sunada yancin zama inda suka ga dama.
Wannan furuci ya fusata fadawan sarkin Yarbawa sun aka fara cacan baki.
KU KARANTA: Diyar Mohammad Indimi zata aure yaron tsohon shugaban kamfanin NNPC
Yayinda gwamnan jihar ya ji wannan abu, ya nada kwamitin karkashin mai basa shawaran kan harkokin gargajiya, Bashir Hussain, domin kashe wannan wuta.
Zaku tuna cewa a shekaran 2017, rikici ya barke tsakanin Yarbawan Ile-Ife da Hausawan da ke zaune a yankin inda akayi asaran rayukan da dama.
Wannan ya sanya sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da sanata Kwankwaso sun kai ziyara garin domin kwantar da kuran.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng