Hukumar Sojin kasa ta bude sabon Bariki a jihar Bayelsa

Hukumar Sojin kasa ta bude sabon Bariki a jihar Bayelsa

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar Sojin kasa ta Najeriya wato Nigerian Army, ta kafa wani sabon barikin soji mai sunan 16 Brigade Camp Buratai a babban birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.

Tsohon Kakakin rundunar sojin, Birgediya Janar Kukasheka Usman, shine ya bayyana hakan a shafin sa na dandalin sada zumuntar facebook, wanda shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya kaddamar.

Shugaban hafsin Sojin ya bayyana farin cikin sa dangane da wannan ci gaba da hukumar ta yi da kuma jinjina ma ta sakamakon kaddamar da wannan Bariki mai dauke da sunan sa da zai shiga cikin kundin tarihi na kasa.

Shugaban hafsin Soji yayin kaddamar da barikin
Shugaban hafsin Soji yayin kaddamar da barikin

Gwamnan jihar Bayelsa yayin kaddamar da barikin
Gwamnan jihar Bayelsa yayin kaddamar da barikin

Buratai yake cewa, tun shekara guda kenan da ta gabata, hukumar sojin take fafutikar assasa wannan bariki, wanda a yanzu ta samu karfi tare da nasarar kafa shi sakamakon jajirce wa da kuma kwazon gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen inganta gudanarwar sojin.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Bikin cikar shekaru 81 na tsohon shugaba Obasanjo

A nasa jawabin, gwamnan jihar Bayelsa Henry Seriake Dickson ya bayyana irin na sa farin cikin dangane da wannan ci gaba, inda ya bayyana cewa gwamnatin sa zata ci gaba da hobbasa da kuma gogayyar kawuna da hukumar sojin kasa wajen ciyar da Barikin gaba.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamna Seriake ya sha alwashin daukar nauyin wasu muhimman gine-gine a Barikin domin nuna irin ruwa da tsakin gwamnatin sa wajen samar da tsaro a kasar nan baki daya.

Jaridar ta Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, anyi arangama tsakani matasan wasu kabilu biyu a jihar Filato da ta salwantar da rayuka uku a ranar Litinin din da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel