Abubuwan da makiyaya suka fadawa Buhari a yayin da ya ziyarci Taraba

Abubuwan da makiyaya suka fadawa Buhari a yayin da ya ziyarci Taraba

- Makiyaya karkashin kungiyar Miyetti Allah na kasa suna nuna jin dadin su bisa ziyarar da shugaba Buhari ya kai jihar ta Taraba

- Makiyayan sunyi kira da shugaban ya gudanar da bincike don gano da hukunta masu hannu cikin kisar tsibirin Mambilla

- Gwamnatin jihar ta Taraba ta nuna gamsuwar kan yadda Buhari ya kawo ziyarar da niyyar samar da zaman lafiya ba wai don a ga fuskar sa ba kawai

Kungiyar makiyaya na Miyetti Allah ta Najeriya ta yi jinjina bisa ga ziyarar da shugaba Buhari ya kai a Jihar na Taraba. Ciyaman din na Arewa maso Gabashin kasa na kungiyar, Alhaji Mafindi Umar, yace ziyarar shugaban kasar zai bunkasa zaman lafiya a tsakanin mutanen Jihar.

Ya kuma yi kira da a gudanar da bincike don ganowa da hukunta wadanda aka samu da hannu a kisar tsibirin Mambilla kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Abubuwan da makiyaya suka fadawa Buhari a yayin da ya ziyarci Taraba
Abubuwan da makiyaya suka fadawa Buhari a yayin da ya ziyarci Taraba
Asali: Twitter

"Ziyarar ta bamu damar fada wa shugaban kasa abubuwan da muke fuskanta, wanda muna fatan da an shirya tsakanin kabilu na jihar za’a samu zaman lafiya.

"Tura Sojoji da Yan Sanda ba shine zai gyara al’amarin ba, amma idan akwai gaskia da adalci, to za’a magance matsalar," inji shi.

KU KARANTA: Gumi ya bayyana hanya daya tilo da sojoji za su bi don cin galaba kan Boko Haram

Bayan haka, Gwamnatin Jihar ta ce, ziyarar tana kara nuna jajir cewar shugaban kasa kan samar da dorariyar zaman lafiya da magance kasha-kashe.

Babban mai taimakawa Gwamna ta fannin sadarwa da jama’a, Mr Bala Dan-Abu, yace ziyarar ta ba wa shugaban kasa damar saurare daga bakin jama’a, Duk da dai wannan shine karo na farko da shugaban kasar yayi jawabi a kan kisan da akeyi a jihar ta Taraba.

"Gwamnatin Jihar Taraba sunji dadin cewar ba wai shugaban kasar ba wai kawai yazo don a ganshi ba ne kadai, amma don samar da mafita ga matsalar da ake fuskan ta," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164